'Yan Iraki na sayar da sassan jikinsu saboda talauci

Image caption Iyalin Om Hussein sun dogar ne da taimako daga wajen 'yan uwa da abokai

Om Hussein, mace ce da ta kusan fitar da rai da rayuwa.

Ita da mijinta da kananan yaranta guda hudu suna fama da talauci kamar wasu miliyoyin 'yan kasar Iraqi.

Mijinta, Ali, ba shi da aikin yi. Yana fama da ciwon suga da ciwon zuciya.

Ita ce take kula da iyalin shekara tara da suka gabata inda ta yi aiki a matsayin 'yar-aiki a wani gida. Amma yanzu ta gaji kuma ba za ta iya aiki ba.

Ms Hussein, a lokacin da take dakinsu da suke zama na wucin gadi a gabashin Baghdad ta ce "Na gaji kuma ba za mu iya samun kudin da za mu biya hayar gidanmu ba da magani da abincin da ma wasu bukatun yaranmu".

Gidan nasu ya rushe a watannin baya amma Allah ya sa sun tsira sakamakon taimako da suka samu daga wajen 'yan uwa da abokai.

Maigidanta ya kara da cewa: "Na yi aiki a duk inda kuke zato, na yi aiki a matsayin mahauci da aikin leburanci da kuma aikin kwasar shara. Bana nema taimakon kudi amma ana bamu; ba zan kuma roki a bani abinci ba.

"Ina sanya yaro na ya tsinto mana ragowar biredi a kan titi mu ci, amma ban taba rokon abinci ko kudi ba."

Matsanancin talaucin da suke fuskanta ne ya sa Ms Hussein ta yi wata sadaukarwa.

"Na yanke shawarar na sayar da koda ta," in ji ta.

"An kai lokacin da ba na iya biya wa iyali ni bukatunsu. Gwara na yi hakan a kan na yi karuwanci ko na yi bara."

Ma'auratan sun tunkari wani mai sayar da koda ba bisa ka'ida ba domin ta sayar da kodarta, sai dai gwajin farko da aka yi mata ya nuna cewa ba za a iya dasawa wani kodar ta ba saboda kodar ba ta da isasshiyar lafiya.

Hakan ne ya sa suka yi tunanin daukar wani mummunan mataki.

Image caption Ali Hussein bashi da aikin yi kuma ya na fama da rashin lafiya
'Kasuwancin sassan jiki'

Matsanancin talauci ya sa safarar koda da wasu sassan jikin mutun sun zama ruwan dare a Bagadaza.

Alkaluman da bankin duniya ya fitar a shekarar 2014 ya ce kusan kashi 23 cikin 100 na mutanen Iraki,wanda yawansu ya kai mutum kusan miliyan 30, suna fama da talauci.

Dillalai suna bayar da har dala10,000 a kan kowacce koda, kuma harin masu fama da talauci da suke yi, ya sa sayar da sassan jiki ya zama hanyar samun kudi a gabas ta tsakiya.

Hukumomi ba za su iya magance matsalar ba saboda ta bazu, in ji Firas al-Bayati, alkali mai fafutukar kare hakkin bil adama.

A shekarar 2012 ne gwamnati ta amince da wata sabuwar doka a wani yunkuri na dakile safarar mutane da sassan jikinsu.

Dangin mutun ne kawai aka yarda su bayar da wani sassan jiki kuma da amincewar wanda zai bayar din.

Masu safarar su kan yi takardun bogi na mai sayen da kuma wanda zai sayar domin su nuna cewa suna da dangantaka.

Tarar da ake cinsu ta danganta, wasu suna shan daurin shekara uku a gidan yari da kuma hukuncin kisa, kuma alkali al-Bayaty ya ce ba sa la'akari da talauci a yarjejeniyar.

Image caption Likitoci sun amince cewar akwai wahala wajen tantance sahihancintakardun mutane
'An samu akasi a kasuwanci'

Da kyar aka bamu damar shiga wani gidan yari da ke Iraki domin ganawa da wani mutun da aka kama yana tayin kodarsa domin a saya.

Bayan mun wuce wurin binciken mutane da ababen hawa da dama, sai muka hadu da Mohammed wanda ya ki ya gaya mana cikakken sunanshi.

'Hoto'

Zai shafe tsawon lokaci a tsare tare da wasu mutane 10 wadanda aka kama da laifin safarar sassan jikin mutun.

Mohammed, mai yara biyu ya ce, "Da farko ban yarda cewa ina da laifi ba. A da, ina yi wa abin kallon agaji ga mutune ne, amma kuma bayan 'yan watanni a cikin wannan kasuwanci sai na fara shakku a kan shi saboda munanan ka'idojin da masu sayar da sassan jikin ke bayarwa. Sai na karaya da na ga yara kanana suna yin wannan harka saboda su samu kudi."

An kama shi a gaban wani asibiti a Bagadaza a watan Nuwambar shekarar 2015 bayan wani dan sanda ya je masa a matsayin wanda zai sayi koda.

A asibitoci masu zaman kansu ake yin akasarin dashen sassan jiki ba a bisa ka'ida ba, musamman a lardin Kurdistan na kasar Iraki, a cewar Mohammed, inda kara da cewa akwai sassaucin takunkumin da aka saka a Bagadaza.

Amma kuma ana iya yin irin wadannan tiyatar a asibitocin gwamnati kamar yadda likitocin suka amince cewar akwai wahala wajen tantance sahihancin takurdun mutane.