Majalisa ta fasa gyara kan dokar da'ar ma'aikata

Image caption Ana tuhumar Bukola Saraki da yin karya wajen bayyana kadarorinsa.

Majalisar Dattawan Najeriya ta ce ta dakatar da shirinta na yin gyara ga dokar hukumar kula da da'ar ma'aikata a kasar.

Majalisar ta dauki matakin ne a daidai lokacin da take shan suka daga wajen 'yan kasar, wadanda ke ganin za su yi gyaran ne domin hana hukumar yin aikinta.

Hukumar kula da da'ar ma'aikatan dai tana tuhumar shugaban Majaliasar dattawan, Bukola Saraki da laifuka 13, wadanda ke da alaka da yin karya wajen bayyana kadarorinsa.

Kazalika, majalisar ta jingine rahoton kwamitinta na da'a kan Sanata Kabiru Marafa, wanda ke jan gaba wajen adawa da Bukola Saraki.