Allon Talla da zai iya yakar kwayar cutar Zika

Allon tallace-tallace mai hallaka sauraye a Brazil Hakkin mallakar hoto Posterscope NBS
Image caption Allon tallace-tallace mai hallaka sauraye a Brazil

Wasu hukumomin tallace-tallace sun kirkiro wani allo da zai rika janyowa tare da hallaka sauraye da yakar cutar Zika a kasar Brazil.

Allon na fitar da wasu sinadarai masu kamshi irin na zufar biladama, da kuma iskar carbon dioxide da ke kunshe a cikin numfashin dan adam din ke fitarwa.

Kanshin jikin allon na iya janyo saurayen daga nisan kilomita biyu da rabi, kamar yadda kamfanonin Posterscope da NBS da suka kirkire shi suka fada.

Kamfanonin sun fitar da hanyoyin da za a bi a kera a kyauta, don karfafawa mutane a fadin duniya da su ma su yi koyi.

Sun kuma yi amanna zai taimaka wajen yakar kwayar cutar Zika wacce sauron ke yadawa.

Yanzu haka sun kafa biyu daga cikin allunan masu kashe sauron a birnin Rio de Janeiro na kasar ta Brazil.

Amma kuma wani kwararre ya yi gargadin cewa zai iya janyo kwarin zuwa yankunan da ke da tarin jama'a.