Shi'a: 'Sojojin Nigeria sun tafka ta'asa'

Hakkin mallakar hoto AP

Kungiyar kare hakkin bil adama ta Amnesty International ta fitar da sabbin rahotanni da ke zargin rundunar sojin Najeriya da yin rufa-rufa game da kashe-kashen mabiya Shi'a a kasar a shekarar da ta wuce.

Kungiyar da kuma wani jami'in gwamnati sun yi zargin cewa sojojin sun kashe sama da 'yan Shi'a fiye da 300 a Zaria a watan Disamba.

Rundunar sojin Najeriya dai ta zargi kungiyar 'yan Shi'an da yunkurin hallaka babban hafsan sojin kasar ne a lokacin wata ziyara da ya kai Zaria, duk da cewa mabiya Shi'a sun musanta wannan zargi.

Rahoton da kungiyar ta Amnesty International ta fitar ya ce akwai wadanda suka gani da idanunsu yadda a cewarsu, sojojin Najeriya suka kona mutane da ransu.

Kungiyar ta kara da cewa, sojojin sun wanke jinin da ya zuba a titi, kuma suka tsince duk harsashe da aka harba, kazalika suka rushe duk gidajen da aka aiwatar da kashe-kashe domin rufe duk wata shaida da za ta sanya su cikin zargi.

Rundunar sojin ta tsaya tsayin daka da cewa sojoji ba su aikata wani abu da ya saba doka ba, kuma ana sauraron wani bincike da gwamnati ke yi domin gano gaskiyar lamarin.