Buhari ya yi wa kasafin kudi gyara

Hakkin mallakar hoto Getty

Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya aike da wata wasika ga majalisar dokokin kasar kan gyare-gyaren da yake son a yi wa kasafin kudin kasar na shekarar 2016.

Shugaban kwamitin yada labarai na majalisar wakilai Hon. Abdulrazak Namdas ne ya tabbatar wa manema labarai hakan ranar Alhamis, inda ya ce majalisar wakilan za ta gana da 'yan majalisar dattijai dangane da batun.

Namdas ya kara da cewa bangarorin majalisar dokokin kasar za su gana su kuma yi aiki game da batun, domin tabbatar da cewa ba a kara daukar lokaci ba an sanya hannun kan kasafin kudin.

Namdas dai bai bayyana wuraren da ke bukatar gyaran ba, amma ya ce za a fayyace wa al'ummar Najeriya nan gaba.

Shi ma mataimaki na musamman ga shugaba Buhari kan harkokin majalisar wakilai, Hon. Kawu Sumaila, ya tabbatar wa da BBC cewa, shugaban ya aike da wasikar ga majalisun dokokin.