China: An dakatar da ayyukan dakin gwaje-gwajen magunguna

Hakkin mallakar hoto Getty

Hukumar hana shan magugunan kara kuzari ta duniya WADA, ta dakatar da dakin gwaje-gwajen magungunan kara kuzari na kasar China har na tsawon watanni hudu.

Hukumar ta ce ta dau matakin ne bayan da dakin gwaje-gwajen ya gaza bin ka'idojin da aka shimfida na kasa da kasa.

Dakatarwar wacce ta fara aiki nan take, za ta haramtawa dakin gwaje-gwajen gudanar da duk wasu ayyuka masu alaka da hukumar ta WADA, kamar bincike kan samfurin fitsari ko jini.

Dakin gwaje-gwajen na da makonni uku na ya daukaka kara kan wannna mataki.

A baya cikin wannan watan ne hukumar ta WADA ta kwace takardar amincewa da dakin gwaje-gwajen magungunan masu saka kuzari na kasar Rasha.

An dakatar da shi a cikin watan Nuwamba bayan wasu zarge-zarge kan rufa-rufa game da amfani da magungunan masu saka kuzarin a Rashar.