Sojin Ethiopia sun gano yaran da aka sace

Image caption Sojojin sun gano yaran da aka sace

Sojojin Ethiopia sun kewaye wani waje a kudancin Sudan inda suka yi amannar ana rike da sama da yara 100 da aka sace.

An sace yaran ne a lokacin wani samame da aka kai a kan iyakar lardin Gambella inda aka yi asarar rayuka 208 a Juma'ar da ta gabata.

Gwamnati ta ce al'ummar Murle ce ke da alhakin satar yaran.

Sa'oi kadan bayan an sanar da harin da aka kai, Firai Minista Hailemariam Desalegn, ya ce gwamnati ta bukaci Sudan ta kudu ta bata damar shiga yankinta domin kamo mutanen da suka kai harin.

Ethiopia da Sudan ta kudu na yin amfani da kan iyaka daya, kuma yin samame a kan iyakar ba wani sabon abu ba ne.

An sauko da tutocin kasar Ethiopia kasa a yayin da da kasar ke alhinin wadanda aka kashe.