Microsoft zai dakatar da kera Xbox 360

Hakkin mallakar hoto Microsoft

Kamfanin Microsoft ya ce zai dakatar da kera na'urar nan da ake amfani da ita wajen sarrafa wasannin komputa, mai kirar Xbox 360.

Shekaru goma da suka gabata ne dai Microsoft din ya kera wannan na'ura ta XBox 360.

A shafinsa na wallafe-wallafe ta intanet jagoran na Xbox Phil Spencer ya ce masu wasan komputar sun kammala ka'idar sa'oi biliyan 78 na wasannnin a kan na'urorin.

Mr Spencer ya kuma ce za a karasa sayar da sauran na'urorin na Xbox 360 da suka rage, za kuma a cigaba da tallafawa bangaren saboda wadanda har yanzu ke amfani da su.

Ya ce akwai wasannin komputa masu kyau da dama da aka yi su musamman don na'urorin Xbox 360 masu sarrafa su, amma kuma sun zama tsohon yayi.