Obama ba ya so Biritaniya ta fice daga EU

Hakkin mallakar hoto PA

Shugaban Amurka Barack Obama ya nuna goyon bayansa kan ci gaba da kasancewar Birtaniya a cikin kungiyar tarayyar turai EU.

Da yake magana a jaridar the Telegraph, Mista Obama ya ce ci gaba da kasancewar Biritaniya a matsayin mambar tarayyar turai, zai kara mata karfin fada-a-ji a duniya.

Ya kuma ce matukar Biritaniyar ta fice daga kungiyar, hakan zai dakushe karfin guiwar da take da shi na yaki da ta'addanci da matsalar 'yan ci-rani.

Tsoma bakin da shugaba Obaman ya yi a kan batun zaben raba-gardama na kungiyar tarayyar turai da za a gudanar a watan Yuni, ya haifar da zazzafar muhawa daga bangaren masu son ballewa daga kungiyar.

Amma a wasu kalaman sa a wata jarida, shugaba Obama ya yi hasashen cewa batun na hannun masu kada kuri'a na kasar Birtaniya na su yankewa kan su da kan su shawara.

Mr Obama dai na yin wata ziyarar aikin kwana uku ne a Biritaniya, a inda zai gana da firai minista David Cameroon, sannan kuma shi da matarsa Michelle za su ci abinci rana da sarauniya Elizabeth wadda ke bikin cika shekara 90 da haihuwa.