Ana bankwana da mawakin nan Prince

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Mawakin dai ya fara tashe ne shekaru kimanin 30 da suka gabata.

Mutane na ta bankwana da shahararren mawakin Amurkar nan aka fi sani da Prince, wanda ya mutu ranar Alhamis yana da shekara 57 a gidansa da ke Minneapolis.

Shugaba Obama ya ce duniya ta yi rashin hazikin mutum mai dimbin basira.

Masoyan Prince dai na ta faman turuwa zuwa gidansa domin yin bankwana da shi.

Mawakin dai ya fara tashe ne shekaru kimanin 30 da suka gabata kuma mutane suna bayyana shi da mawakin da zarta sa'a wajen kirkirar wakoki a zamaninsa.

Mawakin Prince da aka sani da yawan kwalliya, ya soma yin fice ne tun farkon shekarun 1980, inda ya shahara da wakoki irinsu 'I Wanna Be Your Lover' da 'Little Red Corvette'.

Jama'a na yi wa Prince kallon daya daga cikin mawaka masu dimbim basira da kirkire-kirkire iri-iri, inda hadinsa na salon wakar rock da funk da psychedelia ya yi kasuwa, har ya sayar da fayafayai sama da mliliyan dari.

Ya rubuta wa wasu fitattun mawaka wakoki, kuma ya shiga wasu harkokin fina-finai.

Mawakin ya jima yana fama da rashin lafiya, inda har ya kai ga soke wasu gangamin kade-kade biyu da ya shirya yi saboda tsananin mura da aka ce yana fama da ita.