Cikar Sarauniya Elizabeth shekara 90

Hakkin mallakar hoto PA

Sarauniya Elizabeth na bikin murnar kaiwa shekara 90 a wannan makon, kuma babu alamar hutu a gareta.

A bara ta gudanar da ayyuka 306 a Biritaniya, da 35 a kasashen waje.

Wane darasi za mu koya game da koshin lafiya domin samun tsawon rai?

Lafiyayyun kwayoyin halitta
Hakkin mallakar hoto Getty

Sarauniya dai tana iya yi wa mahaifiyarta godiya, wacce ta kai shekaru 101, domin samun ingantattun kwayoyin halitta.

Farfesa Sarah Harper, ta sashen yanayin yadda al'umma ke tsufa, da ke jami'ar Oxford, ta ce fiye da rabin sa'ar samun tsawon rai ya dangana ga kyakkyawar halitta.

Ta ce "Idan kana da iyaye da kakanni da suka kai har shekara 80 ko 90, to akwai damar ka yi gadon kwayoyin halitta masu kyau."

Akwai yiwuwar kuma kana da garkuwar jiki mai karfi, kazalika ba kasafai cututtuka irin su daji ko ciwon zuciya za su kama ka ba.

Ta kara da cewa, "Kwayoyin halitta na iya fito da wasu halaye, kamar shaye-shaye ko yawan cin abinci."

Mahaifin Sarauniya Elizabeth, George na shida, ya rasu yana da shekara 57, kuma kakan ta George na biyar, ya rasu yana 70, amma duk sun rasu sanadiyyar cututtukan da ke da alaka da shan taba ne.

Amma kuma kakar ta ta bangaren mahaifi ta rasu a shekara 85, kuma kakanninta ne gefen mahaifiya, sun kai 89 da 75, kafin rasuwarsu.

Kiyaye munanan halaye

Rabin masu shan taba na mutuwa da wuri, inda suke rasa kusan shekaru 10 a rayuwarsu.

Taba tana sanadin ciwon zuciya da cutar daji ta huhu da matsanancin ciwon fuka.

Sakataren harkokin yada labaran Sarauniyar Dickie Arbiter, ya ce duk da cewa an fi shan taba lokacin da sarauniyar ke yarinya, kuma har mahaifinta da kanwarta na sha a lokacin, ita ba ta taba sha'awar dabi'ar busa taba ba.

Jaridar Vanity Fair ta bayar da rahoton cewa, Yarima Philip ya hakura da shan taba ranar aurensu da Sarauniya, a ganin yadda shan tabar da mahaifinta ke yi ya janyo mata bacin rai matuka.

Hakkin mallakar hoto Getty

Ga alama Sarauniyar ma ba kasafai take shan barasa ba.

Arbiter ya ce, "ba ta shan giya sosai, in ma za ta sha, ba ta wuce kofi daya, da wuya ya kai kofi biyu."

Hukumar kula da lafiya ta Biritaniya, NHS ta shawarci jama'a da cewa kar su sha fiye da kofin giya bakwai a sati, kuma ya kamata su rarraba shi cikin kwanaki uku ko ma fiye.

Hukumar ta gargadi al'umma da cewa barasa na sanadin cututtukan da ke da alaka da zuciya, da hanta da daji na baki da huhu da kuma nono.

Darren McGrady, wanda shi ke dafa wa Sarauniya abinci, ya shaida wa mujallar People Magazine, cewa Sarauniyar na kula da jikinta sosai.

Ya ce in ba dai za ta yi baki ba, bai fi ta ci gasasshiyar kaza da kayan ganye ba, kuma ta horas da kanta ta inda ta hana kanta cin shinkafa, ko dankali ko taliya idan dare ya yi.

Ciwon yawan kitse, da ake samu sanadiyyar rashin cin abinci mai lafiya ko rashin motsa jini, yana rage tsawon rayuwa da shekara 10.

An gano cewa aure na taimakawa wajen samun albarkar shekaru, inda wasu masu bincike a cibiyar binciken lafiya ta NYU Langone Medical Center, suka ce auren da babu matsala na kara lafiyar zuciya, idan aka kwatanta da wanda babu kwanciyar hankali, ko ma wadanda ba su yi aure ba.

Hakkin mallakar hoto Owen Humphreys

Auren Sarauniya da Yarima Philip, wanda ya girme mata da shekara biyar, ya shekara 68.

A shekarar 2012, Sarauniya ta martaba maigidan nata lokacin cika shekara 75, inda ta ce shi ne jagoranta kuma mai ba ta kwarin gwiwa.

Hakkin mallakar hoto Rex

Sarauniyar na motsa jiki kullun saboda ta iya jure wa ayyukan sarauta, kazalika tana dan fita shan iska da karnukanta, ko da safe ko kuma da rana.

Tana kuma tabbatar da cewa ta samu hutawa bayan gwagwarmayar yau da kullun, inda Arbiter ya ce, "Tana samun barcin sa'o'i bakwai a kullun, kuma ana tashinta daga barci da karfe 7:30 na safe."

Sarauniya Elizabeth tana shugabantar fiye da kungiyoyin dauki 600, ciki har da na asibitin Ormond Street da cibiyar binciken cututtukan daji na Biritaniya da kuma hukumar RSPCA, bayan kuma wani bincike da kungiyar Charities Aid Foundation ta gudanar a shekarar 2012, an gano ta taimaka wajen samun tallafin fan biliyan daya da miliyan 400.