Sarauniya Elizabeth II ta cika shekara 90 a duniya

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Mista Cameron ya bayyana Sarauniya Elizabeth a matsayin katangar da ke kare duniya.

Dimbin jama'a ne suka yi dafifi domin taya Sarauniya Elizabeth murnar cika shekaru casa'in a duniya.

Yau da rana makadan badujala sun kada mata taken taya murna.

A majalisar dokoki praminista David Cameron ya jinjina mata kan shekarun da ta kwashe tana jagoranci, da gudunmawar da ta bayar wajen hada kan kasar.

A tsakiyar birnin London an rika harba bindigogi sama, domin taya ta murna.

Sarauniya Elizabeth ta kasance wadda ta fi dadewa kan karagar mulki a tarihin masarautar Birtaniya. Habiba Adamu ta hada mana wannan rahoto.

'Sarauniya, katanga ce'

Image caption Salsalar gidan Sarautar Biritaniya.

Yarima na Wales ya taya mahaifiyarsa, Sarauniyar Biritaniya Elizabeth II, murnar cika shekara 90 a duniya.

Ya yi hakan ne ta hanyar aikewa da wani sako na musamman wanda ya ambato wani bangare na wasan kwaikwayon Henry the Eighth, na fitaccen marubucin nan Shakespeare.

An zabo sakon ne daga wani furuci da Archbishop na Canterbury (Thomas Cranmer) ya yi lokacin da aka haifi Sarauniya Elizabeth ta Farko a shekarar 1533.

Sakon, wanda Yarima Charles ya karanta, yana cewa Sarauniya "za ta kasance matar da kowanne dan Biritaniya da tsofaffin masu sarauta za su ji dadin mulkinta. Za ta dade tanaa gadon sarauta, sannan za ta kwashe tsawon rayuwarta tana mulki na gari."

A sakonsa na taya ta murna, Firai Ministan Biritaniya, David Cameron ya bayyana Sarauniya Elizabeth a matsayin katangar da ke kare kasar da ma sauran sassan duniya.