Samantha Power na ziyara a Nigeria

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Samantha Power a sansanin 'yan hijra a Kamaru

Jakadiyar Amurka a Majalisar Ɗinkin Duniya, Samantha Power, ke fara wata ziyara ta kwana biyu a Najeriya, ranar Alhamis domin janyo hankali kan illar Boko Haram.

Ziyarar dai ci gaba ce ta ziyarar da Mis Power take yi a Afirka, a inda ta kai irin wannan ziyara kasar Chadi da Kamaru, daga ranakun 16 zuwa 20 ga Afrilu.

Yayin ziyarar da ta kai a Kamaru, ta bayyana cewa Amurka za ta bai wa ƙasashen da ke maƙwabtaka da Tafkin Chadi agajin dala miliyan arba'in.

A wata sanarwa da ofishin jakadancin Amurka da ke Abuja, babban birnin Najeriya, ya fitar, Mis Power za ta gana da shugabannin siyasa da kungiyoyin farar hula.

Haka kuma za ta je daya daga cikin sansanonin 'yan gudun hijra a arewa maso gabashin kasar.