Alkali ba zai yi min adalci ba — Saraki

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Ana zargin Saraki da yin karya wajen bayyana kadarorinsa.

Shugaban Majaliasar dattawan Najeriya, Bukola Saraki, ya ce alkalin kotun da'ar ma'aikata ba zai yi masa adalci a shari'ar da kotun ke yi masa ba.

Kotun dai tana tuhumar Bukola Saraki ne da zargin aikata laifuka 13 wadanda ke da alaka da yin karya wajen bayyana kadarorinsa.

Duk yunkurin da shugaban majalisar dattawan ya yi domin ganin kotun ba ta yi masa shari'a ba ya ci tura.

A zaman da kotun ta yi ranar Laraba, lauyan Saraki, Mr Raphael Oluyede, ya zargi shugaban kotun, Danladi Umar, da nuna son kai a shari'ar.

Ya kara da cewa kundin tsarin mulkin Najeriya ya bukaci a bai wa wanda ake zargi da aikata laifuka damar jin ta bakinsa kafin a fara yi masa shari'a, yana mai cewa shugaban kotun bai bai wa Sanata Saraki wannan dama ba.

A cewarsa, hakan ne ya sa ya bukaci Danladi Umar ya janye daga cikin alkalan da ke yi masa shari'a.

Shari'ar dai na ci gaba da jan hankulan 'yan Najeriya.