Tabbas za a cigaba da tattaunawar Geneva - De Mistura

Wakilin musamman na Majalisar Dinkin Duniya a kasar Syria ya ce yana da tabbaci cewa za a cigaba da tattaunawar zaman lafiya a Geneva a makon gobe.

Staffan De Mistura ya nuna damuwarsa da matakin da manyan 'yan adawar kasar Syria suka dauka na saurin ficewa daga zauren tattaunawar.

Mambobin kwamitin tattaunawar sun bar Geneva cikin bacin rai game da hari ta saman da dakarun gwamnati ke kara kai wa.

Amma kuma Mr De Mistura ya bukaci duka bangarorin biyu da su sabunta yarjejeniyar tsagaita wuta, tare da kara agajin jin kai.

A ranar Alhamis ne kwambar manyan motoci dauke da kayan agaji a kasar ta Syria suka isa garin Rastan da 'yan tawaye ke rike da iko.