Amurka ta sayi sinadarin makamai wajen Iran

Hakkin mallakar hoto AP AFP
Image caption Lamarin har ya soma shan suka daga jam'iyyar adawa ta Republican a kasar Amurka.

Amurka na sayen tan 32 na ruwa mai nauyi daga hannun Iran, wanda ake amfani da shi wajen hada sinadaran makami mai linzami.

Gwamnatin kasar ta ce ta saka kudi dala miliyan 8 da dubu dari 6 wajen sayen ne domin kyautata yarjejeniyar nukiliya da suka sanya wa hannu a shekarar da ta gabata.

Jami'ai sunce za a sayar da ruwa mai nauyin da aka saya ga masu bincike, inda ake iya amfani da shi wajen sarrafa sinadaran Plutonium da ake yin makaman Nukiliya da su.

Tuni dai wannan yunkuri ya fara shan suka daga jami'iyyar adawa ta Republican a Amurka, inda kakakin majalisar wakilai Paul Ryan, ya bayyana shi a matsayin "wata dama da ake bai wa kasar da ke gaba-gaba wajen tallafawa kungiyoyin ta'addanci."