Zan dau matakai kan batun tsige ni - Rouseff

Hakkin mallakar hoto c

Shugabar kasar Brazil, Dilma Roussef ta ce za ta nemi kungiyar kasashen Amurka ta Kudu Mercusor ta dakatar da kasar daga kungiyar saboda btaun kokarin tsige ta.

Ms Roussef dai ta sha bayyana matakin tsigeta a matsayin juyin mulki a na siyasa daga abokan hamayyarta da ke neman hambarar da ita.

Kalamam na shugaba Rousseff wasu alamu ne masu karfi da ke nuna cewa za ta ci gaba da kalubalantar yunkurin tsigetan.

Kungiyar ta Mercosur dai na da karfin kakabawa kasashe mambobinta takunkumi masu alaka da rashin tabbas na siyasar kasashen.

Ana dai zargin shugaba Roussef ne da amfani da kasafin kudin kasar wajen neman cin zabe a 2014, zargin da ta sha musantawa.

A makon jiya ne dai 'yan majalisar wakilai ta kasar Brazil din suka kada kuri'ar tsige Ms Rousseff.

Za kuma a iya sauke ta daga kan karagar mulki a cikin makonni masu zuwa idan 'yan majalisar dattawa suka kada nasu kur'i'un.

Batun tsige Rouseff din dai ya haifar da rudanin siyasa da kuma kawo cikas ga gwamnatin kasar ta Brazil.