'Babu kwararan dalilan rage darajar nera'- Buhari

Hakkin mallakar hoto Reuters

A Najeriya, Shugaba Muhammadu Buhari ya ce har yanzu bai sauya ra'ayi ba game da cewa akwai alfanu ga rage darajar kudin kasar Naira, duk da ci gaba da faduwar da ta ke yi kasa da dala a kasuwannin bayan fage.

A wani taro da ya yi da tsoffin ma'aikatan gwamnati, shugaba Buhari ya ce, a shekarun baya, darajar Naira ta na da karfi sosai har sai bayan da aka hambarar da gwamnatinsa a 1985, daga nan ne aka rage darajarta.

Shugaban ya kara da cewa, "To amma da me aka karu da hakan? Ayyuka nawa ne aka samu, kuma masana'antu nawa ne ake gina? Har yanzu dai ni ban ga amfanin sa ba."

Faduwar da farashin mai ya yi a kasuwannin duniya ma ya janyo matsalolin da tattalin arzikin Najeriya bai taba fuskanta ba a shekaru da dama, a matsayin ta na kasar da ke gaba-gaba wajen samar da man fetur, wanda ke samar da kashi 70 cikin dari na kudin shigarta.

Dalar Amurka daya, dai-dai ta ke da Naira 197 a hukumance, amma kuma ya dara haka a kasuwannin bayan fage inda ko a ranar Jumma'a ake sayan kowace dala da nera 320.

A bara ne babban bankin Najeriya CBN ya kaddamar da wasu tsare-tsare, na kare kudaden dake cikin asusun ajiyar Najeriya na kasashen waje, wanda ya yi ramar da ba a taba gani ba a shekaru 11.

Kamfanoni da dama sun yi korafi domin wahalar da suka shiga ta sayen kayan masarufi.

Bankin CBN dai ya yi biris da kiraye-kirayen hukumar bayar da lamuni ta duniya IMF, da masu zuba jari akan ya sassauta tsauraran matakan da ya dauka, matakan da Shugaba Buhari ke marawa baya.