Za a janye mota 600,000 daga Turai

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption An janye motocin kamfanonin ne saboda matsalar hanyoyin fitar iska.

Gwamnatin Jamus ta ce kamfanonin kera motocin Audi da Mercedes da Opel da Porsche da Volkswagen za su janye fiye da motocinsu dubu 600 daga kasuwanni a Turai, saboda wasu kura -kurai da ke tattare da su wajen fitar da hayaki.

Wannan matakin na zuwa ne a yayin da kamfanin Volkswagen ke fuskantar rikicin yin karya game da yawan hayakin da motocinsa ke fitarwa.

Mahukuntan Jamus sun gudanar da gwaji kan motoci daban-daban; inda suka gano kamfanin Volkswagen ne kawai ya saka manhajar da ke rage yawan hayakin da motocin ke fitarwa ba bisa ka'ida ba.

A ranar Alhamis ne kamfanin Volkswagen ya yi tayin sake sayen motocinsa dubu dari biyar a Amurka a wani bangare na yarjejeniyar da suka cimma da ma'aikatar shari'a.