Majalisa za ta gana da Buhari kan kasafin kudi

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Tun dai a watan Disamba ne Buhari ya mikawa majalisar kasar kasafin kudin.

Majalisar dokokin Najeriya ta ce za ta sake wani sabon zama da shugaban kasar, Muhammadu Buhari, domin yin duba kan gyare-gyaren da shugaban ya aikewa da majalisar.

A ranar Alhamis ne dai shugaba Buhari ya aikewa da majalisar wasu gyare-gyare daga cikin kasafin kudin da 'yan majalisar suka amince da shugaban ya sa hannu a kai.

Mai magana da yawun majalisar wakilan kasar, Abdurrazak Namdaz ya ce shugabannin majalisun biyu za su sake gana da Buhari domin jin ta bakinsa dangane da abin da yake son 'yan majalisar su yi.

Sai dai kuma Namdas bai bayyana wuraren da ke bukatar gyaran ba, amma ya ce za a fayyace wa al'ummar Najeriya nan gaba.