An kashe 'yan Boko Haram 27 a Borno

Hakkin mallakar hoto Nigeria Army
Image caption Sojojin sun ce sun kama wasu manyan shugabannin kungiyar ta Boko Haram.

Rundunar sojin Najeriya ta ce dakarunta sun kashe 'yan kungiyar Boko Haram 27 a fafatawar da suka ka yi da 'yan kungiyar a yankuna daban-daban da ke jihar Borno.

Wata sanarwa da kakakin rundunar sojin kasa ta Najeriya, Kanar Sani Kukasheka Usman ya aikewa manema labarai, ta ce dakarunsu, sun kuma kama 'yan kungiyar ta Boko Haram 17.

A cewarsa, an kashe 'yan kato-da-gora biyu da ke yi wa sojojin rakiya.

Kanar Kukasheka ya ce sun ceto mutum kusan 200, kana suka kwato makamai daban-daban daga hannun 'yan kungiyar ta Boko Haram.