Fasahar kare karkanda daga mafarauta

Hakkin mallakar hoto

Kamfanin fasahar tattara bayanai da hadin guiwar kamfanin sadarwa na Cisco, sun fara gwajin fasahar da za ta dakile farautar karkanda a Afirka ta Kudu.

Kamfanonin sun kafa wasu hanyoyin sadarwa na intanet a kusa da wani gandun daji mai zaman kan sa dake daura da gandun dajin Kruger na kasar.

Mataki na gaba kuma zai kasance a hada da kyamarorin tsaro na CCTV, da na'urorin da za su rika sansano tare da dauko hotuna daga nesa zuwa kan intanet din.

Akwai wasu na'urori da ake mannawa a jikin motoci da mutanen da ke shiga gandun dajin, ta yadda za su rika sansano tare da nuna lokacin da suka shiga da kuma abinda ke faruwa.

Wannan tsarin ba don kare karkanda ne kawai ba har ma da sauran dabbobi masu hadari kamar su zakoki, da giwaye da damusa.

Wata kididdiga ta ce akwai yiwuwar bacewar karkanda daga doron kasa nan da shekara ta 2025.

An kuma kiyasta cewa a ko wace shekara ana hallaka karkanda dubu daya don amfani da kahon su.