'Za mu hukunta wadanda suka kashe iyalai 8 a Ohio'

Gwamnan jihar Ohio ta Amurka John Kasich ya lashi takobin cewa za a hukunta wadanda ke da alhakin kisan mutane takwas 'yan gida guda.

Mahukuntan sun bayyana kisan a matsayin wani mummunan kisan gilla.

Wadanda aka hallaka din manya bakwai ne da kuma wani saurayi mai kimanin shekaru 16, kuma dukkanninsu an harbe su a kai ne.

An kuma an gano gawawwakin su a wurare daban-daban har hudu kusa da juna a kan wata hanya.

Kananan yara uku sun tsira daga harbin - daya daga cikinsu jariri ne mai kwanaki hudu da haihuwa da aka samu kwance kusa da gawar mahaifiyarsa.

Jami'an tsaro a yankin Pike dake gabashin Cincinnati sun ce suna kan farautar wadanda suka aikata kisan.

Wani Fada dake wurin da lamarin ya faru ya ce kisan zai iya yiwuwa ne an aikata shi ne sakamakon wasu matsaloli na cikin gida.