Sulhu kan rikicin kamfanin Arik

Hakkin mallakar hoto BOEING MEDIA
Image caption Ana bin kamfanin jiragen sama na Arik bashin naira biliyan 12

Gwamnatin Najeriya ta tsoma baki cikin takaddamar da ta kaure tsakanin kamfanin zirga-zirgar jirage sama mafi girma a kasar wato Arik, da kuma kungiyoyin ma'aikatan sufurin jiragen sama kan bashin naira biliyan 12 da kungiyoyin suka ce suna binsa.

A ranar Laraba ne wakilan kungiyoyin suka hana jiragen kamfanin tashi daga filin jirgin saman Legas babban birnin kasuwanci na kasar kan wannan bashin,abin da ya sa fasinjoji da dama suka kasa yin tafiya.

Kasancewar kamfanin ya musanta zargin kungiyoyi ,ministan sufurin kasar Hadi Sirika ya shaidawa Haruna Tangaza cewa sun bai wa kungiyoyi hakuri kana sun shiga tattaunawa da kamfanin domin gano gaskiyar lamarin, ga dai yadda hirar ta su ta kasance;

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti