Bangladesh: An kashe malamin jami'a

Image caption Marigayi Farfesa Karim SIddique

Ɗaruruwan dalibai a garin Rajshahi na arewa maso yammacin Bangladesh sun yi zanga-zanga a harabar jami'a dangane da kisan malaminsu Farfesa Rezaul Karim Siddique.

Wasu da ake zaton masu ikirarin kishin musulunci ne suka kashe malamin jami'ar yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa aiki.

An bada rahoton cewa, ƙungiya mai alaƙa da IS ce ta dau alhakin kisan malamin jami'ar.

Amma gwamnatin Bangladesh ta musanta kasancewar ƙungiyar IS a ƙasar.

'Yan sanda sun ce, wanda aka kashe ɗin Farfesa Siddique ba shi da abokan gaba, kuma ba ya ƙalubalantar addini.

Amma 'yan sandan sun ce, kisan ya yi kama da salon kisan da aka yi wa wasu marubuta da ba ruwansu da addini, da kuma ɗalibai.

Shi dai marigayin malami ne a sashen nazarin harshen Turanci na jami'ar Rajshahi.