Alaƙar Boko Haram da IS a tafkin Chadi

Hakkin mallakar hoto AFP BOKO HARAM
Image caption Boko Haram sun kashe dubban mutane

Rahotanni na cewa akwai alaka ta musayar makamai tsakanin Boko Haram a tafkin Chadi da kungiyar IS a kasar Libya.

Tun dai bayan hambarar da shugaban Libya, Muammar Gaddafi, makamai suka yawaita a hannun 'yan tawaye wadanda kuma ake zargin su ne suke kwarara zuwa hannun Boko Haram a yankin tafkin Chadi.

Rundunar hadin gwiwa ta kasashen da ke kewaye da tafkin Chadi wato Multinational Joint Task Force, ta ce ba ta da isassun dakarun da za su iya yin sintiri a kan iyakokin yankin na tafkin Chadi saboda girmansu.

Amma kuma manjo Janar Lamidi Adeosun wanda shi ne kwamandan rundunar, ya shaidawa BBC cewa dakarun rundunar na ci gaba da ayyukan kawar da Boko Haram daga yankunan da ke kewaye da Tafkin Chadi kamar yadda aka tsara.

Sai dai kuma mista Adeosun ya ce har yanzu kasar Benin ba ta turo da nata dakarun da ta yi alkawarin bayarwa ga rundunar ba.

Rundunar hadakar dai ta kunshi dakaru ne daga kasashen Najeriya, Nijar, Kamaru da Chadi.