Yarjejeniyar cinikayya tsakanin EU da Amurka

Hakkin mallakar hoto Getty

Dubban jama'a suna zanga zanga a birnin Hanova a Jamus domin nuna adawa da shirin yarjejeniyar cinikayya tsakanin turai da Amurka wadda aka fi sani da T-TIP a takaice.

Masu adawa sun ce yarjejeniyar za ta raunana matakan kare muhalli da kuma hakkin ma'aikata.

Sai dai shugaba Obama yace yarjejeniyar za ta samar da guraben ayyuka miliyan daya, sannan shawarar ragin kudin fito zai habaka cinikayya a daidai lokacin da tattalin arzikin duniya ke cikin halin rashin tabbas.

A ranar Lahadi ne ake sa ran Obama zai kai ziyara Hanover inda zai bude babbar kasuwar baje koli da kuma tattaunawa da shugabannin tarayyar turai.

A ranar litinin kuma ake fatan ci gaba da shawarwari a kan jadawalin yarjejeniyar a birnin New York