Nigeria: Za a karfafa kananan masa'anantu

A Najeriya an bayyana kanana da kuma matsakaitan masana'antu da kasuwanci a matsayin wasu hanyoyin da za su rage rashin ayyukan yi da zaman kashe wando.

An bayyana haka ne a wurin wani taro na kawanaki 3 da hukumar kula da kanana da matsakaitan kafafen sanya jari ta Nigeria SMEDAN ke yi a Kaduna.

Hukumar ta ce, ta na duba hanyoyi ne na bunkawa da gyara ayyukan ta domin warware matsalar talauci da zaman kashe wando tsakanin matasa.

Ana wannan taro ne a yayin da masu masana'antu kanana da matsakaita ke fama da wasu matsaloli kamar na jari da wadatar wutar lantarki.

Gwamnati dai ta ce ta na daukar matakai na warware irin wadannan matsaloli.