Ana cigaba da kashe fararen hula a Syria

Image caption Mutane goma sha uku sun mutu sakamakon hare-hare ta sama a Syria

Rahotanni daga Syria na cewa an kashe fararen hula da dama sakamakon hari ta saman da dakarun gwamnati suka kai wuraren da 'yan tawaye ke rike da su.

Wata kungiyar kare hakkin dan-adam ta Syrian Observatory for Human Rights, ta ce an kashe fararen hula goma sha uku wadanda suka hadar da mata da yara a harin da aka kai a garin Douma da ke kusa da Damascus.

Kazalika kamfanin dillancin labaran Faransa ya rawaito cewa an kashe wasu fafaren hula goma sha biyu a rana ta biyu da kai hare-hare a arewacin birnin Aleppo.

Amurka da Majalisar dinkin duniya sun bayyana cewa akwai alamun da ke nuna cewa ana samun karuwar tashe-tashen hankula a Syria, abinda ke karasa damuwa a kan cewa da wuya a cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a kasar.