Yuguda: Dalilansa na fita daga PDP

Tsohon gwamnan jihar Bauchi a Nigeria, Malam Isa Yuguda ya yi karin haske akan dalilansa na fita daga jam'iyyar adawa ta PDP.

A wata hira ta waya da manema labarai tsohon gwamnan ya ce, ya fita daga jam'iyyar ne saboda abinda ya kira ƙazantar dake cikinta.

Malam Isa Yuguda ya kuma ce, ci gaba da zakulo abubuwan da ba daidai ba da aka aikata a lokacin mulkin PDP na daga cikin dalilansa na fita daga jam'iyyar.

Tsohon gwamnan ya ce, yadda ake tafiyar da jam'iyyar a yanzu ya saɓa ƙa'ida.

Wannan dai shi ne karo na biyu da Malam Isa Yuguda yake ficewa daga jam'iyyar PDP.

Ya zama gwamnan jihar Bauchi a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar ANPP a shekara ta 2007.

Amma tsohon gwamnan ya sake komawa jam'iyyar PDP daga bisani.

Yanzu dai bai bayyana jam'iyyar da zai koma ba, amma ya ce, yana tuntuɓar magoya bayansa.