An soma zabe a Equatorial Guinea

Shugaba Teodoro Obiang Hakkin mallakar hoto
Image caption Shugaba Teodoro Obiang

Masu zabe a kasar Equatorial Guinea sun soma kada kuri'a a zaben da ake ganin shugaban kasa da ya fi dadewa kan mulki a Afrika ne zai sake yin nasara.

Shugaba Teodoro Obiang shi ne ya ke rike da mulki a kasar da keda arzikin man fetur a yammacin Afrika, tun bayan da ya yi wa kawunsa juyin mulki a shekarar 1979.

'Yan takara 6 ne zasu fafata da shugaba Obiang sai dai manyan jam'iyyun adawa sun ce zasu kauracewa zaben.

Mista Obiang bai taba samun kuri'u kasa da kashi 95 cikin dari a zabukan da aka yi a can baya ba.

An bayana kasar ta Eqautorial Guinea a matsayin daya daga cikin kasashen duniya da matsalar cin hanci da rashawa ta yi wa katutu, kuma kasa ce da bata mutunta dokokin kare hakin bil'adama.

Duk da dimbim arzikin man fetur din da take da shi, akasarin alummar kasar na rayuwa ne akan kasa da dala biyu a kowace rana.