Kalubalen ziyarar Obama a Jamus

Hakkin mallakar hoto Getty

Shugaban Amurka Barack Obama ya fara ziyara a Jamus tare da kudirin shawarwari na cinikayya tsakanin turai da Amurka wadda ake yiwa lakabi da T-TIP a matsayin jigon batutuwan ziyarar.

Gabanin ziyarar dai Ministan tattalin arzikin Jamus Sigmar Gabriel ya yi gargadin cewa yarjejeniyar T-TIP za ta rushe idan Amurka ba ta amincewa kamfanonin turai damar neman kwangiloli na gwamnati ba.

A ranar Asabar dubban jama'a sun gudanar da zanga zanga a Hanover inda Obama zai yada zango a ziyarar ta kwanaki biyu.

Mr Obama yace yarjejeniyar za ta samar da guraben ayyuka da kuma habaka cigaban tattalin arziki.

Sai dai wani wakilin BBC a Berlin yace Obama na da jan aiki a gaba wajen shawo kan jama'a a kan batun.