'Mutane miliyan 2 sun rasa muhallinsu a Najeriya'

Yan gudun hijira a Najeriya
Image caption Wasu 'yan gudun hijira a sansanin NEMA

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Najeriya wato NEMA ta ce mutane kusan miliyan biyu ne suke zaune a sansanonin 'yan gudun hijira daban -daban a jihohin Borno da Yobe da Gombe da Taraba da Bauchi da kuma Adamawa.

Jami'in NEMA mai kula da sansanin 'yan gudun hijira dake birnin Yola, Sa'ad Bello shi ne ya sanar da haka lokacin da jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya Samantha Powers ta ziyarci sansanin na Malkohi a jihar Adamawa.

Ya ce akwai wasu sansanoni 32 a jihohin Borno da Yobe da kuma Adamawa wadanda mutane sama da 189,000 da suka rasa muhalinsu suke samun mafaka

Malam Bello ya ce jihar Borno tana da sansanoni 19, wadanda 'yan gudun hijira sama da 150,000 suke samun mafaka, jihar Yobe kuma tana da sansani tara inda mutane sama da 31,000 suke samun mafaka yayin da jihar Adamawa ke da sansani hudu inda mutane sama da 6,000 suke samun mafaka.

Madam Samantha ta ce ta kai ziyara sansanin Malkohi ne domin ta ga yadda Amurka za ta taimakawa Najeriya wajen murkushe mayakan Boko Haram domin 'yan gudun hijira su koma gidajensu