Yadda gwamnatoci ke murkushe shafukan zumunta

Hakkin mallakar hoto
Ana samun karuwar gwamnatocin Afirka da ke toshe kafofin sada zumunta da muhawara a lokacin zabuka.Clare Spencer ya nemi jin dalilin da ya sa ake yin hakan da kuma yadda jama'a suke ji:Mai ya sa gwamnatocin Afirka ke toshe kafofin sada zumunta da muhawara?

Binciken da hukumar tuntuba kan harkokin siyasa da yada labarai ta Portland Communication ta gudanar ya nuna cewa masu rubutu a shafin Twitter a nahiyar Afirka sun fi karkata ga harkokin da suka shafi siyasa fiye da sauran masu amfani da Twitter daga wasu nahiyoyi.

Kuma gwamnatoci na toshe kafofin sada zumunta da muhawara a lokacin zabuka-musamman na baya-bayan nan a kasashen Congo-Brazzaville da Chadi da kuma Uganda.

Idan ka kalli boren da ya faru a kasashen Larabawa, za ka ga irin tasirin da kafofin sada zumunta da muhawara ke yi a harkokin siyasa.

Arthur Goldstuk daga kamfanin Worldwide Worx da ke yin bincike, ya fada wa BBC cewa ba kafofin sada zumunta da muhawara ne suka janyo boren da aka yi a kasashen Larabawa ba, amma sun taimaka wajen shirya shi.

Gwamnatoci ba su ce sun damu cewa kafofin sada zumunta da muhawara ka iya share hanyar gudanar da wata zanga-zanga ko ma juyin juya hali ba.

Amma a wasu lokuta ana duba batun tsaro - da suka hada da bai wa kamfanonin wayar salula umarnin su katse layukansu a kasar Congo-Brazzaville.

Jami'an kasar Congo sun kara da cewa suna kokarin hana wallafa sakamakon zabe wanda ba na hukuma ba ne.

Jaridar Newsweek ta fassara hakan a matsayin wani yunkuri na dakile kokarin masu sa ido a kan zabe.

Wayar salula ta bai wa kungiyoyin sa ido damar tattara sakamako daga daidaikun rumfunan zabe a kewayen kasar da kuma tara su domin ganin ko an tafka magudi wajen tattara sakamakon.

Idan da a ce wayoyin salula ba sa aiki, da hakan ba zai yiwu ba.

Sai dai ba lallai ba ne sakamakon zaben da jam'iyyun adawa suke fitarwa daidai ne kuma Shugaban Uganda Yoweri Museveni ya hakikance cewa an toshe kafofin sada zumunta da mahawara a lokacin zabe domin a hana yada karairayi.

Ta yaya gwamnatoci suke katse kafofin sada sumunta da mahawara?

Thecla Mbongue, mai sharhi ce a bangaren sadarwa da kafofin yada labaru, ta kuma yi bayanin cewa gwamnatoci ba sa iya toshe shafukan intanet da katshe wayoyi ko kuma toshe wani abu da aka rubuta da kansu.

Suna yin hakan ne ta hanyar bai wa kamfanoni umarni wadanda su ne ke da ikon yin hakan.

Gwamnatin Congo-Brazzaville ta fitar da wata oda ga kamfanonin wayar salula irinsu Airtel da kuma MTN.

Ms Mbongue ta ce umarnin da Congo-Brazzaville ta fitar ga alamu ya bai wa wasu mutane ne kawai damar ci gaba da amfani da wayoyinsu na salula.

Wannan ya fito ne lokacin da ministan sadarwa ya yi watsi da cewa an tashe hanyoyin sadarwa- ta hanyar rubutu a shafinsa na Twitter.