An harbe wani kwamandan sojin Burundi

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Rikici ya barke a Burundi ne tun da Shugaba Pierre Nkurunziza ya lashi aniyar yin ta-zarce.

Wasu 'yan bindiga sun harbe wani Kwamandan sojin Burundi tare da matarsa har lahira, a bujumbura, babban birnin kasar.

An harbe Janar thanase Kararuza a lokacin da yake kan hanyar kai 'yarsa makaranta ranar Litinin da safe.

Ma'aikatar tsaron kasar ta tabbatar da kashe Janar Kararuza.

Kwamandan shi ne na baya bayan nan da aka kashe tun bayan barkewar rikici a kasar sakamakon sake tsayawa takara a karo na uku da Shugaba a shekarar da ta wuce.

A ranar Lahadi ma, ministan kare hakkin dan adam Martin Nivyabandi ya tsallake rijiya da baya a lokacin da aka tayar da wasu gurneti a daidai lokacin da yake fita daga wata Coci.