Za a yi wa Donald Trump taron-dangi

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Donald Trump ya ce abokan hamayyarsa sun karaya.

A kasr Amurka, masu son yi wa jam'iyyar Republican takarar shugabancin kasar su biyu Ted Cruz da John Kasich sun amince su hada kai domin yi wa abokin takararsu Donald Trump taron-dangi.

Shi dai Trump shi ne ke kan gaba a dukkan zabukan fitar da gwanin da aka gudanar ya zuwa yanzu.

Sai dai Ted Cruz ya sha alwashin zai taimaka wa Mr Kasich domin ya lashe zaben fitar da gwani na jihohin Oregon da New Mexico yayin da Mr Kasich zai taimaka wa Cruz wajen lashe jihar Indiana.

Mr Trump ya bayyana abokan hamayyarsa a matsayin mutanen da suka yi "matukar kagara, wadanda kuma ba za su kai labari ba.

Mr Trump yana bukatar kuri'a 1,237 domin samun tikitin yi wa jam'iyyar Republican takara, kuma rashin samunsu zai iya sa wa manyan jami'an jam'iyyar su zabi dan takarar da suke so, ko da ba shi ne ya samu kuri'u mafi rinjaye ba.