Masar: An murƙushe yunƙurin zanga-zanga

Hakkin mallakar hoto AFP

'Yan sanda da sojojin Masar sun yi murkushe wani yunkuri na yin zanga-zangar nuna adawa da gwamnati a birnin Alƙahira.

Jami'an tsaron sun yi amfani da hayaƙi mai sa hawaye wajen tarwatsa 'yan kalilan din mutanen da suka samu damar yin gangami domin zanga zangar.

Wasu kungiyoyi da suka fusata da matakin gwamnatin kasar na miƙa wasu tsibiri ga Saudiyya ne suka kira zanga-zangar.

Sai dai kuma baya ga wannan jama'a sun ƙosa da yadda tattalin arziƙin kasar yake tangal-tangal.

Masu nazari sun ce, matakin murƙushe zanga zangar alama ce ta kaɗuwar da shugaba Abdul Fattah Al Sisi ya yi.