"Mata ne ke sa maza cin hanci"

Hakkin mallakar hoto AFP

Masu rajin kare hakkin mata a Indonesia sun soki wani minista saboda ya ce kwadayayyun mata ne ke sa mazajensu ke karbar cin hanci a wuraren ayyukansu.

Ministan harkokin addini, Lukman Hakim Saifuddin, ya fada wa mahalarta wani taro cewar, a wasu lokutan maza ba sa jin dadin rashin kasancewa tare da iyalinsu, don haka su kan so su ba su kyaututtuka domin su kwantar musu da hankali.

Hakim ya ce hakan yana tunzura mazan su karbi kudi ta hanyar cin hanci.

Mista Saifuddin ya bukaci mata su daina tirsasawa mazansu su ba su kyaututuka masu tsada, wadanda ba su da kudin sayensu, domin a shawo kan matsalar.