Tsohon dan Majalisar Kogi zai sha daurin shekaru 154

Hakkin mallakar hoto efcc website

Wata babbar kotun gwamnatin tarayya dake Lokoja a jihar Kogi ta sami Gabriel Daudu da aikata laifuka 77 sannan aka yanke masu hukuncin daurin shekaru 154 a gidan yari.

Wannan na dauke ne a ckin wata sanarwa da hukumar nan dake yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagwon kasa EFCC ta fitar dauke da sa hannun kakakinta Wilson Uwujaren.

Sanarwar ta bayyana cewa hukumar EFCC ta sami nasarar samun wani tsohon dan majalisar dokokin jihar Kogi kuma tsohon Shugaban riko na karamar hukumar Ogori/Magongo na jihar Gabriel Daudu da laifin zambar kudi Naira biliyan 1.4

A watan Afrilun shekarar 2010 ne hukumar EFCC ta soma gurfanar da Daudu kan zarge zarge 208, da suka danganci halartar kudaden haram da kuma barnatar da kudaden al'umma.

Mai shari'ah Inyang Ekwo wanda ya jagoranci shari'ar a wata babbar kotun gwamnatin tarayya dake Lokoja a jihar Kogi, ya same shi da aikata laifuka 77, sannan aka yanke masu hukuncin daurin shekaru 154 a gidan yari

Kafin a yanke masa hukuncin mai gabatar da kara Wahab Shittu ya gabatarwa da kotun shaidu guda 13 da za su tabbatar da tuhumar da ake masa