Mexico: An tono bayanai akan masu jefa ƙuri'a

Hakkin mallakar hoto PA

Wani mai binciken harkar tsaro a Amurka ya gano yadda aka sanya dukkan bayanai akan masu jefa ƙuri'a miliyan 87 na ƙasar Mexico a Internet.

Bayanan sun hada da ranar haihuwa, adireshi, da kuma lambar katin jefa kuri'a na mutanen miliyan 87 'yan ƙasar Mexico da suka yi rajistar jefa ƙuri'a.

Wanda ya gano waɗannan muhimman bayanai Chris Vickey yana shiga shafukan internet inda yake ƙoƙarin gano bayanai muhimmai da aka bari a bainar jama'a.

Koda a kwanakin baya an saka bayanan masu jefa ƙuri'a miliyan 70 na kasar Philippines a Internet.

Barin irin waɗannan bayanai na baiwa masu satar bayanai damar aikata zamba da kuma satar muhimman bayanan jama'a.