Za a hana bara a Sokoto

Hakkin mallakar hoto Getty

Gwamnatin Sokoto da ke arewacin Nigeria ta sanar da shirye-shiryen da take yi na hana bara a a fadin jihar.

Mataimakin gwamnan jihar, Alhaji Ahmad Aliyu wanda ya sanar da hakan, ya ce gwamnati za ta samar wa da mabaratan ayyukan da za su rika yi domin su kasance masu dogaro da kansu.

Alhaji Ahmad Aliyu ya ce gwamnati ta dauki wannan mataki ne domin a kawar da talauci da kuma rashin aikin yi a tsakanin mutane.

Ya kara da cewa, "Shirin zai tabbatar da cewa an wadatar da dukkanin abubuwan da suka zama wajibi ga mabukata tare da cikakken goyon bayan gwamnatin jihar".

Mataimakin gwamnan ya ce wannan ita ce hanya kadai da za a cimma kudurorin da alkawuran da gwamnati ta dauka, a matakin jiha da kuma na gwamnatin tarayya