'Mutum 438,000 Maleriya ke kashewa'

Hakkin mallakar hoto

A ranar Litinin ne ake bikin ranar yaki da cutar zazzabin cizon sauro, watau Malaria ta duniya.

Majalisar dinkin duniya ce ta kebe wannan rana a duk shekara domin matsa kaimi wajen kawar da cutar.

An kiyasta cewa mutane 438,000 ne ke mutuwa duk shekara sanadiyyar kamuwa da cutar, sannan mutane miliyan 214 na kamuwa da cutar.

Kashi 90 cikin 100 na masu kamuwa da cutar a nahiyar Afirka suke.

Mutane da dama ne ke fuskantar barazanar kamuwa da cutar a duniya muddin ba a dauki wani mataki ba.

Taken ranar ta bana dai shi ne 'Kawo Karshen Maleriya don Samun Alheri'.

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO dai ta ce kasashen Turai sun cimma burin kawar da cutar zazzabin na cizon sauro tun a bara.

Amma har yanzu cutar na mummunar barna a kasashe masu tasowa.