Buhari ya gana da shugabannin majalisa

Shugaban Nigeria, Muhammadu Buhari ya gana da shugabannin majalisar dattijai da kuma ta wakilai domin warware takaddamar da ta kunno kai a tsakaninsu game da kasafin kudin kasar na 2016.

Shugaba Buhari dai ya mayar da kasafin kudin ga majalisar dokokin domin su yi wasu gyare-gyare kafin ya sanya masa hannu.

Sanata Ali Ndume, wanda ya halarci ganawar ya shaida wa BBC cewa an samu fahimtar juna tsakanin bangarorin biyu:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ndume ya ƙara da cewa, an kafa kwamitin da zai warware sabanin da ke tsakanin ɓangarorin biyu dangane da kasafin ƙudin.

'Yan majalisar dokokin dai sun bayyana aniyarsu ta ganin an kammala gyara kasafin kudin cikin mako guda.