Yadda karancin ruwan sha ke addabar Indiya

A inuwa ma, zafin garin ya kai ma'aunin celcius 42, amma kuma hakan bai hana Anjali Patole ta hau layin dibar ruwa ba kullun a wurin wani tankin ruwa a wani dakali mai zafi sosai a birnin Latur da ke yammacin jihar Maharashtra.

Anjali da kawunta da mahaifinta sun yi hijira zuwa garin Pune domin su samu aikin yi kuma mahaifiyarta ta na sayar da kayan lambu. Ta kan tsaya cikin rana har tsawon sao'i uku domin ta cika wasu abubuwan dibar ruwa guda 15.

Sun shafe watanni uku ba su da ruwa a fanfo. Bayan kowadanne kwanaki takwas ne motar daukar ruwa da ke zuwa kwaryar birnin ke zuwa titin gidansu ta raba litar ruwa 200 ga kowanne gida.

Anjali ta ce, ruwan ba ya taba isar gidansu, a saboda haka ne Anjali take amfani da lokacin hutun makarantarta tana debo musu ruwa. Baka tsoron zafi zai yi mata illa? Tambayar kenan da na yiwa kawunta.

'Dole Ne'

A farkon wannan makon ne wata yarinya mai shekara 12 ta rasa ranta sakamakon zazzabi mai zafi bayan ta shafe sa'oi hudu tana dibar ruwa daga wata rijiyar tuka-tuka a wata gundunmar Beed da ke makwabtaka. Anjali ta riga ta yi sa'oi biyu a lokacin da na hadu da ita.

Kawun nata sai ya yi watsi da tambayar da na yi masa.

Ya ce "dole, dole" a lokacinda yake 'yan guna-guni. " Ba mu da wani zabi."

Rashin isashen ruwa na saka mutane su shiga wani hali na rashin zabi. Mazauna Latur, na daga cikin mutane miliyan 330 a gundumomi 256 a Indiya da ke fama da fari sakamakon shekara uku da aka shafe ba ruwan sama.

Dalilin da yasa mutane rabin miliyan da ke cikin birnin gundumar ba su da wata rayuwa sai ta neman ruwan da za su yi amfani da shi. Suna damuwa sosai a kan inda za su samu ruwa da kuma tsananin tunani a kan zabin da su ke da shi na ruwa.

Zan jira ne har sai motar da ke raba ruwa ta zo ko kuwa na bi layi? Ko kuma na duba rijiyar tuka-tukar da ke kan titi? A gida ma babu wani sauki a zabin da suke da shi.

Na kara yin wanka ne a wannan zafin da ake fama da shi? Na dafa abinci da baya bukatar a yi amfani da ruwa sosai? Na gayyaci mutane su zo su ci abincin dare? Na dage ranar da za a yi min tiyata saboda na adana kudin da zan sayi ruwa?

Yakin da ake zaton za a yi wajen neman ruwa a karni na 21 ya riga ya dabaibaye hankulan mutane a nan. Birnin cike yake da jita-jita da zargi.

Ko kansilan kwaryar birnin ya sa an kai motocin ruwa zuwa garuruwan da ke mazabarsa? Ko makwabci na yana bai wa direban motar ruwan cin hanci don ya basu ruwa?

Ciwon zuciya yayi sanadiyar mutuwar matar da ta ke aikin sa kai na kula da layin dibar ruwa da kuma wata mata da ta shafe sa'oi da dama a layin dibar ruwan a sakamon tsananin rikicin da ake fama da shi kan ruwa.

Mutane suna dambe a kan layin dibar ruwan.

A watan da ya gabata ne dai hukumomi suka hana taron mutane da yawa a wajen dibar ruwa saboda a kawar da yawan fadace-fadacen da ake yi.

'Sabon abinda aka yi sabo da shi'

An sha yin zanga-zanga a wajen tankunan da ake tara ruwa wanda ya ja hankulan hukumomi suka saka kofofi masu kaya a matattakala domin hana hawa wajen cikin hanzari.

Mutane har 20 da suka yi fada a kan dibar ruwa sun kai kara Ofishin 'yan sanda da ke cikin birnin.

Duk zafin yanayi da ake fama da shi a dare ma, dogon layi ne a wurin wani tankin adana ruwa a cikin tsakiyar birnin.

Ba kowa a kan tituna, amma dandamalin da ake dibar ruwan cike yake da mutane ana ta hada-hada.

'Yanayi mai wuya'

Hukumomin suna ikirarin cewa motocin daukar ruwa 125 suke kai ruwan sha gidaje kullum.

Babban jami'i a Latur, Pandurang Pole, ya gaya min cewa a lokacinda aka yi fama da matsanancin rashin ruwa a watan Fabrairu, birnin na samun kashi hudu cikin lita miliyan 25 na ruwansu.

Shekara biyu da aka shafe ana fama da rashin ruwan sama isasshe ya jawo ruwan kogin Manjara ya ragu sosai wanda yake bai wa Latur ruwa.

Mista Pole ya ce " a yanzu birnin na kokarin cike gibin ta hanayar samar da ruwa lita miliyan 20 ta kowacce hanya da ta samu.

Ana farfado da madatsan ruwa guda biyu, da rijiyoyi 150 da kuma kokarin farfado da wani shirin samar da ruwa da kuma jirgin kasa na ruwa.

" Yanayi ne mai wahala sosai, "inji shi. Muna da ruwan da zai ishe mu har zuwa watan Yuli kuma muna fatan samun ruwan sama wannan shekarar."

A wajen garin abubuwa sun fi kyawun gani

Motocin daukar ruwa suna bai wa kauyuka 150 ruwa daga cikin kauyuka 800.

Zurfin ruwan da ke kasa ya kai zurfin kafa 500(mita 152). Mazauna kauyukan na haka rijiyoyi suna neman ruwa.

Noma kayayyakin da ake sayarwa wadanda ake shukawa wajen fadama kamar irinsu rake da auduga sun shafe shekaru basa samun isashen ruwa a gundumar da ke da yawan mutane miliyan 4.5.

Manoma wadanda bashi ya yi musu katutu sun kashe kansu a wannan shekarar.

Duk da haka ana fatan samun sa'ida a birnin.

Mutane sun jure kuma sun yi hakuri matuka duk da dai 'yan siyasa suna lika fastar jimi'yyunsu a kan tankunan ruwa inda suka dauki alhakin samar da jirgin kasa na ruwa.

'Abin kunya'

Idan muka dan kauce daga hayaniya, mutanen garin wadanda gidauniyar Art of Living su ke karfafa musu guiwa, ta bada gudunmawar miliyan 30 na rupee domin a haka kogin Manjara na gundunmar tsawon kilomita 18. Masu haka 20 ne suke aiki ba dare ba rana domin su kammala aikin.

Kafewar kogin abin kunya ne ga mutanen Latur, in ji Mahadev Gomare na kungiyar. Allah ya bamu ruwa, kamata ya yi mu kula da shi."

Wani manomi matashi wanda ya sayi rijiya domin ya rika ban ruwa a gonarsa kuma ya shuka masara, ya yanke shawarar ya bai wa mutanen kauyen ruwa kyauta na tsawon sa'a biyu kullum da yamma. " abinda za mu shuka za su iya jira" a cewar Vikas Manikrao Sul wani alkali mai shekara 31.

Ya ce bai wa iyalan da wannan abin ya shafa ruwa ya fi muhimmanci. A lokacin da ake fama da rashi kar a yi tunanin ribar da za a samu."

Dole Latur zai dauki tsawon lokacin yana tanda da kuma samar da ruwansa da kyau, kuma ya canza yanayin noma domin ya kaucewa aukuwar irin wannan bala'in. Amma kafin sannan, sai an yi ruwan sama sosai.