Kano: Gobara ta tashi a kasuwar Kurmi

Image caption Kasuwar Sabon Gari ma ta fuskanci gobara

Rahotanni daga birnin Kano a Nigeria na cewa wata gobara da ta tashi a Kasuwar Kurmi, ta ƙona aƙalla shaguna 30.

Rahotannin sun ce 'yan kwana-kwana sun ci ƙarfin gobarar, wacce ta tashi da daren ranar Talata.

Wani shaida ya ce 'yan kasuwa sun yi ta kwashe kayansu daga shagunansu.

Ko da a ƙarshen watan Maris, mummanar gobara ta haddasa asarar dimbin dukiya a kasuwar Sabon Gari da ke Kano.

A watan Fabrairu ma, wata gobarar ta haddasa gagarumar ɓarna a kasuwar Singa ita ma a Kano.

Sarkin Kano Muhammadu Rumfa ne ya kafa kasuwar Kurmi cikin ƙarni na 15.

A wancan lokacin kasuwar ta kasance babbar cibiyar hada-hadar kasuwanci a yankin hamadar Sahara.

Kasuwar mai shekaru fiye da 600 asali cibiya ce ta cinikin bayi, kuma tana cikin kasuwanni mafiya jimawa a yankin Afirka ta yamma.