Sakamakon binciken kisan 'yan kallon Liverpool

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption 'Yan kallon sun mutu ne a filin wasa a arewacin Ingila a 1989.

A binciken da aka dade ana jiran sakamakonsa a Biritaniya, masu taya alkali yanke hukunci sun zartar da cewa, 'yan kallon kwallo 96 da suka mutu a turmutsitsi a Hillsborough, akwai saba doka a mutuwar tasu.

'Yan kallon sun mutu ne a filin wasa a arewacin Ingila a 1989.

Binciken na shekaru biyu ya gano cewa matakin da 'yan sanda suka dauka bayan turmutsutsin ya taimaka ga mace-macen.

Binciken ya ce bai kamata a zargi halayyar magoya bayan ba.

Iyalan wadanda abin ya shafa sun zubar da kwalla a kotun yayin da ake bayyana sakamakon.