Nijar: An kama masu kokarin tsallakawa Algeria

Hakkin mallakar hoto
Image caption Hukumar kula da kaura ta duniya ta ce a shekarar da ta gabata mutane 100,000 ne suka ketara Algeria daga Nijar.

Hukumomi a Jamhuriyar Nijar sun ce sun kama 'yan kasar sama da 100, a lokacin da suke kokarin tsallakawa zuwa makwabaciyar kasar Aljeriya daga jahar Agadez.

Rahotanni sun ce galibin mutanen mata ne da kanana yara kuma 'yan asilin yankin Kantche ne a jahar Damagaram.

Shi dai wanan yanki na Kantche ya yi kaurin suna wajen tururuwa da mata ke yi tare da kananan yara zuwa kasar Aljeriya.

Hukumar kula da kaura ta duniya ta ce a shekarar da ta gabata mutane 100,000 ne suka ketara Algeria daga Nijar din ta jihar Agadez a kan hanyar su zuwa Turai.