Sudan ta Kudu: Machar ya koma kan mukaminsa

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Dangantaka ta yi tsami tsakanin Salvir Kiir da Riek Machar.

An rantsar da Reik Machar a matsayin sabon mataimakin shugaban kasar Sudan ta kudu bayan ya koma Juba, babban birnin kasar.

Mista Machar ya koma Juba bayan ya kwashe mako guda yana jan-kafa lamarin da ya kusa yin kafar-ungulu ga shirin zaman lafiyar kasar.

Machar ya karbi mukamin ne a wani bangare na yarjejeniyar da aka kulla domin kawo karshen yakin basasar da aka kwashe shekara biyu ana yi a kasar, wanda ya yi sanadiyar mutuwar dubban mutane, sannan ya raba kimanin mutane miliyan biyu daga gidajensu.

Ya shaida wa manema labarai a filin jirgin saman Juba cewa ya dawo birnin ne domin a zauna lafiya.

Mista Machar ya tsere daga Juba a lokacin da aka fara yakin a watan Disambar shekarar 2013.

Gwamnatin kasar ta zarge shi da yunkurin juyin mulki, ko da ya ke ya musanta - kuma hakan ya kara jefa kasar cikin mummunan yaki.