Likitoci na yajin aiki a Biritaniya

Hakkin mallakar hoto
Image caption Kananan likitoci za su kauracewa duba marasa lafiya.

A ranar Talata ne kananan likitoci a Biritaniya ke fara yajin aikin gama-gari a karon farko a tarihin tsarin kiwon lafiya na kasar.

Kananan likitoci za su kauracewa duba marasa lafiya, da ma masu bukatar kulawar gaggawa saboda sabanin da ke tsakaninsu da gwamnati dangane da bullo da sabon tsarin aiki.

Masu gudanar da bangaren kiwon lafiyar sun ce an yi kyakkyawan tsari domin tabbatar da cewa marasa lafiya ba su fuskanci kunci ba.

Sai dai za a sa ido a ga irin tasirin da yajin aikin zai yi.