Iraqi: Gwamnati ta dakatar da Al Jazeera

Gwamnatin Iraqi ta umarci kafar yada labarai ta Al Jazeera da ta rufe ofishinta na birnin Bagadaza, tare da hana ma'aikatanta bayar da rahotanni a kasar.

Hukumomin sun zargi kafar yada labaran da karya dokar kafefen yada labarai ta kasar Iraqi, da suka hada da haramta yada duk wasu ayyukan kungiyoyin masu tada kayar baya.

Al Jazeerar ta ce ta kadu matuka game da wannan mataki, kana ta musanta karya duk wata doka da ta shafi aikin kafafen yada labaran.